Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya ɗansa, Seyi Tinubu, murnar naɗa shi sarautar gargajiya ta Dan Zakin Gwandu da Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya yi masa a Jihar Kebbi.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an ce an gudanar da bikin naɗin ne a ranar Laraba a fadar Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi.

Shugaban ƙasar ya gode wa Sarkin Gwandu da majalisar masarautar bisa wannan karramawa, wadda sarkin ya bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin masarautar.

Ya ce sarautar tana ɗauke da nauyin da ya wuce karramawar mutum, domin tana nuna zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummar Najeriya.

Tinubu ya yaba wa ƙoƙarin ɗansa wajen hulɗa da matasa, bunƙasa al’umma da ƙarfafa matasa, musamman ta hanyar ƙungiyar City Boy Movement da sauran shirye-shiryen tallafa wa matasan Najeriya.

A cewarsa, sarautar Dan Zaki Gwandu, wadda ke nufin ɗan zaki na Gwandu, tana ɗauke da darussan jarumtaka, shugabanci da hidimar al’umma.

Ya buƙaci ɗansa da ya kasance mai tawali’u tare da sadaukar da kansa wajen taimaka wa jama’a.

Shugaban ƙasar ya ƙarfafa Seyi da ya ɗauki sarautar a matsayin ƙarin nauyin da zai ƙarfafa jajircewarsa wajen bunƙasa matasa, zaman lafiya da yi wa Najeriya hidima, tare da yi masa fatan samun hikima da ƙarfin guiwa wajen sauke nauyin da ke tattare da ita.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *