Ma’aikatan Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Shehu Idris da ke Makarfi a Jihar Kaduna, sun shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai saboda rashin biyan wasu kaso na albashinsu da kuma wasu buƙatun jin daɗin ma’aikata.
Kwamitin haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadago na makarantar (JAC) ne ya ayyana yajin aikin, bayan wa’adin kwanaki 15 da ya bai wa gwamnatin Jihar Kaduna ya ƙare.
Shugaban kwamitin, Goma Umar Farouq, ne ya sanar da matakin a wani taron manema labarai da aka gudanar a Makarfi ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, 2026.
Farouq ya ce matakin ya biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin gazawar gwamnatin jihar wajen mayar da martani ga wasiƙu da tunatarwa da kuma roƙon da kwamitin ya aika mata, domin ganin an biya ma’aikatan haƙƙoƙinsu na albashi da sauran alawus-alawus.
Ya bayyana cewa kwamitin ya rubuta wa gwamnati sau da dama, ciki har da wasiƙar roƙo ta musamman, da wasiƙun tunatarwa guda biyu, sannan ya ba ta wa’adin kwanaki 15, wanda ya ƙare ranar Laraba.
A cewarsa, ba da sauƙi aka yanke shawarar shiga yajin aikin ba, sai dai hakan ya zama dole bayan ƙoƙarin da suka yi na ganin an tattauna matsalolin tare da samun maslaha ya ci tura.
- Sojojin Nijar 319 sun bayar da gudunmuwar jini kyauta a Yamai
- ’Yan sanda sun ƙwato wayoyi 222 da sauran kayayyakin sata a Kano
Farouq ya ce manufar matakin ita ce kare ingancin ilimi a Jihar Kaduna, tabbatar da biyan ma’aikata albashi yadda ya kamata da kuma inganta jin daɗin ma’aikatan manyan makarantu, musamman ta kwalejin.
Daga cikin buƙatun kwamitin akwai biyan ragowar kashi 30 cikin 100 na tsarin albashin ma’aikatan lafiya na COMPASS/CONTEDISS da kuma tsarin albashin ma’aikatan manyan makarantu na CONTISS ga ma’aikatan da abin ya shafa.
Haka kuma, kwamitin na buƙatar gwamnatin jihar ta aiwatar da ƙarin alawus-alawus na kashi 25 da kashi 35 cikin 100 da gwamnatin tarayya ta amince da su, waɗanda ya ce an riga an fara biya a wasu manyan makarantu a faɗin ƙasar.

Sauran buƙatun sun haɗa da aiwatar da tsarin albashin malamai na CONTTA da na ma’aikatan da ba malamai ba na CONUASS, gwargwadon waɗanda suka shafa, tare da biyan dukkan bashin da ya taru sakamakon sauye-sauyen albashi da alawus-alawus ɗin.
Kwamitin ya kuma buƙaci gwamnatin jihar ta fitar da takardar sanarwar hukuma kan sauya shekarun ritayar ma’aikatan da ba malamai ba, ta yadda za a riƙa yin ritaya ne idan ma’aikaci ya kai shekara 65 ko kuma ya yi shekaru 40 yana aiki, duk wanda ya fara zuwa.
Shugaban kwamitin ya ce sun yi ƙoƙarin warware matsalolin ta hanyar tattaunawa sau da dama, yana mai cewa ba yajin aikin ne zaɓinsu na farko ba, amma sun ga ya zama dole domin jawo hankalin gwamnati kan halin da mambobinsu ke ciki.

Ya ce bayan shawarwari da tattaunawa, majalisar ƙungiyoyin ƙwadagon makarantar ta amince da fara yajin aikin gargaɗin na kwanaki bakwai, wanda ya fara aiki daga ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba.
Farouq ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kaduna da ta gaggauta duba buƙatunsu domin dawo da zaman lafiya tsakanin ma’aikata da mahukunta, inganta walwalar ma’aikata da kuma ci gaban manyan makarantu a jihar.