Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da fasa shaguna huɗu a kasuwar wayoyin hannu ta City Centre Plaza, da ke Farm Centre, tare da ƙwato dukkan kayayyakin da aka sace.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Nuwamba, 2026, bayan jami’an tsaro na kasuwar sun kai rahoton fasa shagunan ga ofishin ’yan sanda na Farm Centre.

Ya ce jami’an ’yan sanda sun garzaya wurin tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron kasuwar, inda suka kama wanda ake zargin yana yawo a cikin kasuwar da abin yanka ƙarfe da sukandireba, amma ya kasa bayar da gamsasshen bayanin dalilin kasancewarsa a wurin.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa laifin fasa shagunan huɗun da satar kayayyaki.

Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai kwamfutar Lenovo guda ɗaya, kwamfutar hannu ta Samsung, wayoyin maɓalli 95, wayoyin Android 127 da na’urorin sauti.

Sauran kayayyakin sun haɗa da inverter, allunan wayar hannu guda 17, na’urorin sarrafa hasken rana, power bank 29, belun kunne 15, kayan haɗin waya 130 da kuma kuɗi Naira 350,000.

Rundunar ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *