Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum da ake zargi da yi wa mata fyade, musamman zawarawa, tare da ɗaukar bidiyonsu ba tare da izininsu ba.
Rundunar ta ce wanda ake zargin na amfani da bidiyon wajen yi wa matan barazana, tsoratar da su da kuma yi musu baƙar fata domin tilasta musu yin abin da yake so.
- NCDC ta ce ba a samu sabon rahotun cutar Ebola ba cikin makonni uku
- CAF ta sauya ranar bikin bayar da kyaututtukan CAF Awards na 2026
A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.