Najeriya da ƙasar Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin tsara gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 da kuma tabbatar da walwalar alhazan Najeriya.
Shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, da mataimakin ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Abdulfattah Bin Sulaiman Mashat, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Jeddah.
Sanarwar da shugaban sashen yaɗa labarai na NAHCON, Shafii Sani Mohammed, ya fitar ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi rabon kujerun Hajjin da Najeriya za ta samu, bin dokokin Saudiyya da wa’adin kammala shirye-shirye.
Haka kuma, yarjejeniyar ta tanadi tsarin masauki, sufuri, kula da lafiyar alhazai da sauran hidimomin da suka shafi gudanar da aikin Hajji.
Ambasada Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa zuba jari a kayayyakin more rayuwa da inganta hidimomin alhazai, tare da tabbatar da aniyar NAHCON na yin aiki tare da hukumomin ƙasar domin inganta aikin Hajjin ’yan Najeriya.
A nasa ɓangaren, Dakta Mashat ya ce kashi 93 cikin 100 na alhazai sun nuna gamsuwa da hidimomin da aka ba su a Hajjin 2026.
Yanzu NAHCON za ta yi aiki da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da masu shirya aikin Hajji masu lasisi domin aiwatar da yarjejeniyar da kuma kammala shirye-shiryen Hajjin 2027 cikin lokaci.