Akalla sojojin Nijar 319 sun bayar da gudunmuwar jini a wani shiri da Cibiyar tattara jini ta ƙasar (CNTS) ta gudanar a makarantar horas da sojoji da ke ƙauyen Tondibia, kusa da birnin Yamai.

Cibiyar ta ce jimillar sojoji 358 ne suka miƙa kansu domin bayar da gudunmuwar jinin, amma an samu nasarar karɓar jinin mutum 319.

Wannan mataki na nuna yadda jami’an tsaron Nijar ke bayar da tasu gudunmuwar wajen ceton rayukan al’umma, ta hanyar taimaka wa waɗanda ke buƙatar ƙarin jini a asibitoci.

Bayar da gudunmuwar jini na daga cikin hanyoyin ceton rayuka, musamman ga marasa lafiya da waɗanda suka samu munanan raunuka sakamakon haɗurra ko wasu matsaloli na lafiya.

Masana lafiya da masu wa’azi na ƙarfafa al’umma su riƙa bayar da gudunmuwar jini domin rage ƙarancinsa da kuma taimakawa wajen hana mutuwar mutanen da ke buƙatar ƙarin jini cikin gaggawa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *