Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da takardar murabus ɗin da aka ce tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Nafiu Bala, ya rubuta, bayan ta gano cewa sa hannun da ke jikin takardar ya bambanta da nasa.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce takardar da ɓangaren jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya dogara da ita wajen tabbatar da murabus ɗin Bala ba sahihiya ba ce.

Alƙalin ya bayyana cewa bayan kwatanta sa hannun da ke jikin takardar da waɗanda ke cikin bayanan shaidar da Bala ya gabatar a kotu, ya gano bambance-bambance masu muhimmanci. Saboda haka, ya ce takardar ba za ta zama hujjar cewa Bala ya yi murabus da kansa ba.

A cewar kotun, kasancewar an tabbatar da sahihancin kwafin takarda ba ya nufin an tabbatar da sahihancin sa hannun da ke jikinta. Alƙalin ya ce ya kamata kotu ta tantance irin wannan takarda tare da sauran hujjoji kafin yanke hukunci.

Bala dai ya shigar da ƙara tun watan Satumban 2025, inda ya ƙalubalanci shugabancin David Mark da na sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola. Ya sha musanta rubuta takardar murabus ɗin, yana mai cewa an ƙirƙira ta ne tare da sa hannun da ba nasa ba.

Hukuncin ya kuma soke sahihancin zaɓen Mark da Aregbesola a taron kwamitin zartarwa na ƙasa na ADC da aka gudanar a 27 ga Yuli, 2025, bisa rashin bin ƙa’idojin zaɓen shugabanni da dokar zaɓe ta 2022 ta tanada.

Wannan mataki ya ƙara dagula rikicin shugabancin jam’iyyar da kuma shirye-shiryenta na zaɓen 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *