’Yan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kammala haɗuwa a sansaninsu da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom, yayin da dukkan ‘yan wasa 24 da aka gayyata suka isa, gabanin wasan neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2027 da za su fafata da Tanzania a ranar Juma’a.
Isowar ‘yan wasan da suka rage ta sa kocin tawagar, Eric Chelle, ya samu cikakkiyar tawaga gabanin atisaye na biyu, yayin da Najeriya ke shirin fuskantar muhimman wasanni biyu da tawagar Taifa Stars ta Tanzania.
Cikakkiyar tawagar ta kunshi kyaftin Wilfred Ndidi, Ademola Lookman, Alex Iwobi, Calvin Bassey, Ola Aina, Moses Simon da Tolu Arokodare, tare da sauran ‘yan wasan gab ana tawagar.
-
CAF ta sauya ranar bikin bayar da kyaututtukan CAF Awards na 2026
-
Atiku ya taya Flamingos murnar lashe Kofin Duniya na mata ’yan ƙasa da shekara 17
-
Najeriya ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya bayan doke Japan 2-1
Sauran ‘yan wasan da ke sansanin sun hada da masu tsaron raga Stanley Nwabali, Francis Uzoho da Arthur Okonkwo. Haka kuma akwai ‘yan wasan baya Semi Ajayi, Bright Osayi-Samuel, Benjamin Fredrick, Chibuike Nwaiwu, Abdullahi Bewene da Bruno Onyemaechi.
A ɓangaren ’yan wasan tsakiya, akwai Alhassan Yusuf, Tochukwu Nnadi, Samson Tijani, Fisayo Dele-Bashiru da Suleiman Mubarak. Yayin da Akor Adams, Taiwo Awoniyi da Moses Usor suka kammala jerin ‘yan wasan gaba na tawagar.
Super Eagles za ta karbi bakuncin Tanzania a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, kafin ta tafi Zanzibar domin buga wasan zagaye na biyu a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.
An tsara fara wasan farko da karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya.
Najeriya na fuskantar matsin lamba na samun dukkan maki ukun da ake nema, bayan da ta fara wasannin neman gurbin da nasarar doke Madagascar da ci 2-1, kafin daga bisani Guinea-Bissau ta lallasa ta da ci 3-0.
Wadannan sakamakon sun sa Najeriya wacce ta lashe gasar nahiyar Afirka sau uku suna da maki uku kacal, maki uku a bayan Guinea-Bissau wadda ke jagorantar rukunin.
A daya bangaren kuma, Tanzania ta riga ta samu tikitin shiga gasar AFCON ta 2027, kasancewar tana cikin kasashen da za su karbi bakuncin gasar. Hakan na nufin Najeriya da sauran kasashen da ke rukunin L za su fafata ne domin neman tikitin shiga gasar guda daya da ya rage.
