Aure yana buƙatar amana, biyayya da mutunta juna. Saboda haka, shiga rayuwar aure yana nufin ɗaukar sabon mataki na sadaukarwa, tare da kafa iyakoki da za su taimaka wajen kare zaman lafiya da amincewa tsakanin ma’aurata.
Ko da yake kowa yana da tarihin soyayya kafin aure, bai kamata tsoffin alaƙa su zama sanadin rikici ko rashin fahimta a sabon zaman aure ba. Yin watsi da wasu abubuwan da suka shafi tsoffin masoya na iya taimakawa wajen gina kyakkyawar dangantaka.
Ga abubuwa shida da ya kamata mutum ya yi la’akari da su bayan aure kamar yadda Jaridar Pulse Ghana ta wallafa:
Goge hotuna da bidiyon sirri: Bai dace mutum ya ci gaba da riƙe hotuna, bidiyo ko saƙonnin soyayya na sirri da ya yi musayar su da tsohon masoyinsa ba. Irin waɗannan abubuwa na iya jawo zargi da rashin amana, tare da karya sirrin mutanen da abin ya shafa.
Goge lambar tsohon masoyi idan babu dalilin riƙe ta: Idan babu wata muhimmiyar alaƙa ta aiki ko wani nauyi da ke buƙatar sadarwa, riƙe lambar tsohon masoyi na iya buɗe ƙofar sake farfaɗo da tsohuwar alaƙa.
- Tinubu ya taya ɗansa murnar naɗa shi Dan Zaki na Masarautar Gwandu
- Najeriya ta kammala gasar Olympics na matasa na Dakar 2026 da tarihi mai kyau
Guji amfani da laƙabin soyayyar da aka yi wa tsohon masoyi: Laƙabin soyayya kan kasance da tarihin musamman a zuciyar mutum. Saboda haka, yana da kyau a samar wa sabon abokin aure wani suna na musamman da zai nuna darajarsa a rayuwar aure.
Daina bibiyar tsohon masoyi a kafafen sada zumunta: Yawan duba shafukan tsohon masoyi, sa ido kan rayuwarsa ko bibiyar sababbin alaƙarsa na iya hana mutum mayar da hankali kan sabon gidansa. Yana da muhimmanci a bar baya a baya.
Guji ganawa da tsohon masoyi a ɓoye ba tare da dalili ba: Ganawa da tsohon masoyi a keɓe, musamman idan har akwai sauran sha’awa ko alaƙar zuciya, na iya jefa aure cikin matsala. Ya kamata a kiyaye iyakoki domin kauce wa rashin fahimta.
Kasance mai gaskiya idan tsohon masoyi ya sake neman hulɗa: Idan tsohon masoyi ya sake tuntuɓar mutum da niyyar farfaɗo da tsohuwar alaƙa, yana da kyau kada a ɓoye hakan daga abokin aure. Bayyana gaskiya da kafa iyakoki na taimakawa wajen ƙarfafa amana.
Jaridar ta ƙara jaddada cewa aure yana buƙatar mutum ya mayar da hankali kan sabon abokin rayuwarsa, tare da girmama juna da kiyaye abubuwan da za su iya kawo barazana ga zaman lafiyar gidansa.