Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya da su tabbatar da kare haƙƙin kowane yaro a ko’ina cikin duniya.
UNICEF ta ce shekaru 37 da suka gabata, shugabannin duniya sun yi alƙawarin kare yara, taimaka musu wajen samun ilimi da kuma tabbatar da ’yancinsu na faɗin albarkacin bakinsu da sauraron ra’ayoyinsu.
- ’Yan sandan Imo sun horas da jami’ai 500 kan ƙwarewa da mutunta haƙƙin jama’a
- Majalisar Wakilai ta amince da kudurori uku kan asibitoci, ɓarkewar zazzabin cizon sauro da OPay
Ta bayyana cewa an yi wannan alƙawarin ne ta hanyar yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan haƙƙin yara, wadda ta ce ita ce yarjejeniyar kare haƙƙin bil’adama da ƙasashe suka fi amincewa da ita a tarihi.
A saƙonta na bikin Ranar Yara ta Duniya, UNICEF ta buƙaci shugabannin ƙasashe da su cika wannan alƙawari ta hanyar kare haƙƙin dukkan yara, ba tare da la’akari da inda suke zaune ba.