Mataimakin Shugaban Hukumar Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Anthony Oluwatosin Ogunjimi, ya nemi ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin hukumar da Hedikwatar Tsaron Najeriya domin tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin Afirka ta Yamma.
Ogunjimi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, yayin wata ziyarar sanayya da ya kai Hedikwatar Tsaron Najeriya da ke Abuja, inda Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, ya tarbe shi.
Mataimakin shugaban hukumar ya yaba wa Najeriya kan gudunmawar da take bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin, musamman rawar da dakarun sojin ƙasar suka taka a ayyukan wanzar da zaman lafiya a Laberiya, Saliyo, Gambiya da Guinea-Bissau.
- Sojoji sun kashe ɗan ta’adda, sun kama uba da ɗansa bisa zargin alaƙa da Lakurawa a Sakkwato
- UNICEF ta bukaci shugabannin duniya su cika alƙawarin kare haƙƙin yara
Ya bayyana cewa jajircewar Najeriya wajen haɗin gwiwar tsaro na daga cikin muhimman ginshiƙan ƙoƙarin ECOWAS na haɗa kan ƙasashen yankin da tabbatar da zaman lafiya.
Ogunjimi ya kuma yaba wa shugabancin Hedikwatar Tsaron Najeriya kan ƙoƙarin kare iyakokin ƙasar, tare da bayyana muradin ECOWAS na faɗaɗa dangantakarsu ta fuskar haɗin gwiwar tsaro, tattaunawar dabarun aiki da sauran shirye-shiryen tunkarar sabbin barazanar tsaro a yankin.
A nasa jawabin, Janar Oluyede ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa, amincewa da juna da ɗaukar alhakin tsaro tare tsakanin ƙasashen ECOWAS.
Ya kuma buƙaci ƙasashen yankin su ƙarfafa alaƙar sojojinsu da yin aiki tare domin cimma manufofin ƙungiyar.