Ƙasar Belgium ta bayyana cewa akwai yiwuwar Iran ce ke da hannu a hare-haren kutse ta intanet da aka kai kan na’urorin sanyaya kayayyaki na manyan shagunan sayar da abinci a ƙasar a cikin wannan wata, kwanaki kaɗan bayan Faransa ta zargi Tehran da hannu a irin wannan lamari da ya faru a watan Oktoba.

Ministan Harkokin Cikin Gida na Belgium, Bernard Quintin, ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa bayanan da hukumomin ƙasar suka tattara sun nuna yiwuwar Iran ce ke da hannu a harin, sai dai bai kai ga tabbatar da cewa ita ce ta aikata hakan a hukumance ba.

Tun da farko a jiya Alhamis, Ministan Harkokin Wajen Belgium, Maxime Prevot, ya bayyana cewa zai zama gaggawa a hukumance a jingina alhakin harin kutse ta intanet ga wata ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa manyan shagunan sayar da abinci da dama a faɗin Belgium sun fuskanci matsalar na’urorin sanyaya kayayyaki a ranar 2 ga watan Nuwamba, lamarin da ya tilasta wa wasu shagunan zubar da abincin da suka lalace.

Haka kuma, an samu irin wannan matsala a wasu shaguna da ke ƙasashen Estonia, Finland, Ireland, Italiya, Luxembourg, Netherlands, Portugal da Sweden.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *