Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta wallafa sunan Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Ogun na jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na shekarar 2027, cikin sa’o’i 24.
Mai shari’a Peter Lifu, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da wata jam’iyyar siyasa ta tsayar bisa ƙa’ida, ba tare da izinin kotu ba.
Alƙalin ya ce matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin mulki, ya saɓa wa doka kuma ba shi da wani inganci.
Mai shari’a Lifu ya bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ko babbar kotun jiha ce kaɗai ke da ikon ayyana cewa ɗan takara bai cancanta ba, ba INEC ba.
- ’Yar takarar mataimakiyar gwamnan NDC a Cross River ta fice daga jam’iyyar
- Jami’ar UNN ta tabbatar da mutuwar ɗalibai huɗu, wasu shida na kwance a asibiti
- Yara sama da 17,000 sun kamu da cutar nimoniya a Kano – Kwamishina
Ya kuma ce hukumar INEC ta tauye wa Adebutu haƙƙinsa na samun adalci a shari’a, kafin ta cire sunansa daga jerin ‘yan takara ba tare da bin ƙa’ida ba.
Alƙalin, wanda ya yi watsi da ƙin amincewa da ƙarar da INEC ta shigar tun farko, ya bayyana cewa ƙarar ta cancanci sauraro a gaban kotu.
Jam’iyyar PDP da Adebutu sun shigar da ƙarar ne a ranar 22 ga watan Oktoba, bayan da aka cire sunan Adebutu daga jerin masu neman kujerar gwamnan jihar Ogun.
Masu ƙarar sun shigar da INEC a matsayin wanda ake ƙara shi kaɗai, ta hannun lauyansu, Ahmed Raji, SAN.
Masu ƙarar sun gabatar da tambayoyi shida domin kotu ta yanke hukunci a kansu, tare da neman a ba su umarni guda 11.
Sun nemi kotun ta soke matakin hukumar na ƙin saka sunan Adebutu ko cire shi daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar da ta wallafa a ranar 10 ga watan Oktoba, bisa dalilin tauye masa haƙƙin sauraro da kuma karya tanade-tanaden sashe na 29 da na 32 na dokar zaɓe ta shekarar 2026.
Haka kuma, sun nemi kotun ta umarci INEC da ta saka ko wallafa sunan Adebutu a cikin sa’o’i 24 da bayar da hukuncin, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar Ogun a babban zaɓen shekarar 2027, tare da wasu buƙatu.