Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai wa wasu tarukan siyasa a sassan Najeriya, tare da kira ga hukumomin tsaro su kamo waɗanda ke da hannu a ciki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar kamfen ɗin, Dele Alake, ya fitar ranar 12 ga Nuwamba, 2026, APC ta ce hare-haren da aka ruwaito a jihohin Edo, Cross River da Gombe, da kuma waɗanda aka kai wa magoya bayan jam’iyyu da ’yan siyasa, abin Allah-wadai ne.
Jam’iyyar ta kuma yi Allah-wadai da tarwatsa wani taron tattaunawa da jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta shirya gudanarwa a Legas a ranar 12 ga Nuwamba.
- UNICEF ta bukaci shugabannin duniya su cika alƙawarin kare haƙƙin yara
- Shugaban Iran ya kammala ziyarar aiki a Turkiyya bayan halartar taron COP31
- Sanarwar ta buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu su guji duk wani mataki da ka iya haddasa rikici ko tayar da tarzoma yayin da ake ci gaba da kamfen ɗin zaɓe.
APC ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara sa ido tare da ɗaukar matakan da suka dace domin hana tashin hankalin siyasa, da kuma kamo waɗanda suka haddasa ko suka aikata hare-haren domin hukunta su bisa doka.
Ta ƙara da cewa ya kamata jam’iyyun siyasa da ’yan takara su mayar da hankali kan gabatar da manufofin da za su inganta rayuwar ’yan Najeriya, maimakon tayar da zaune tsaye a wajen tarukan siyasa.