Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa an gano yara sama da 17,000 da ke fama da cutar nimoniya a jihar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin bikin tunawa da Ranar Cutar Nimoniya ta Duniya da Ranar Ciwon Suga ta Duniya da aka gudanar a Kano ranar Laraba, ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan al’umma kan cututtukan biyu da hanyoyin kariya, gano su da wuri da kuma samar da magani.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar, kwamishinan ya ce a bana kadai, cutar nimoniya ta shafi yara sama da 300,000 a faɗin Najeriya.
- Amupitan ya amince zaɓen 2023 ya rage amincewar ’yan Najeriya ga INEC
- INEC za ta gwada na’urorin BVAS a faɗin Najeriya ranar 28 ga Nuwamba
- Majalisar Wakilai ta ware Naira miliyan 100 ga ’yan wasan Flamingos bayan lashe Kofin Duniya
Ya yi gargaɗin cewa cutar na da haɗari ga yara, musamman ƙanana, sannan rashin isasshen abinci mai gina jiki na ƙara yiwuwar kamuwa da ita da tsananta yanayin masu fama da ita.
Dakta Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta horas da ma’aikatan lafiya kan hanyoyin kula da cututtukan yara, domin inganta jinya da tabbatar da cewa yaran da suka kamu da cutar sun samu kulawar da ta dace.
Game da cutar suga, kwamishinan ya ce sama da mutane miliyan 500 ne ke rayuwa da ita a duniya, yayin da kimanin kashi 7.5 cikin 100 na al’ummar Jihar Kano ke fama da cutar. Ya jaddada muhimmancin bin shawarwarin likitoci domin kauce wa matsalolin da cutar ka iya haifarwa.
Ya ƙara da cewa cibiyoyin lafiya sama da 1,000 a jihar sun amfana da rabon kayan aikin jinya da gwamnatin Kano ta yi, domin inganta gwajin gano cutar suga da kulawa da masu fama da ita.
Ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan kariya, gano cututtuka da wuri da kuma inganta jinyarsu.