Wani bincike da aka gudanar a ƙauyen Damau da ke Jihar Kaduna ya gano cewa shanu a yankin na samar da lita 1.2 kacal na nono a kowace rana, lamarin da ke nuna ƙarancin amfanin da ake samu daga kiwon shanu a yankin.

 

Binciken, wanda ya ƙunshi gidaje 730, an gudanar da shi ne ƙarƙashin Shirin Samar da Matsugunan Makiyaya da Jure Sauyin Yanayi a Najeriya.

 

Bincike, ya danganta ƙarancin nonon da tsoffin hanyoyin kiwo, rashin ingantattun dabarun zaɓen bijimai da kuma ƙarancin amfani da hanyoyin zamani na samar da nono.

Binciken ya gano cewa shanun Fulani farare ne suka fi yawa a yankin, yayin da ba kasafai ake kiwon shanun da aka shigo da su daga ƙasashen waje ba.

 

Haka kuma, gidaje tara cikin 10 na da aƙalla dabba guda ta kiwo, yayin da kusan kashi 59 cikin 100 ke aikin samar da nono, kashi 52 cikin 100 kuma ke sayar da shi domin samun kuɗin shiga.

 

Masu binciken sun bayyana cewa shanun gida irin su farare na iya samar da lita 12 zuwa 15 na nono a rana idan aka inganta yadda ake kula da su.

 

Sun kuma ce shanun nono da aka shigo da su daga ƙasashen waje, waɗanda ake kiwonsu bisa ingantaccen tsari, na iya samar da kusan lita 30 a rana, kamar yadda rahoton Arla Farm Open Day Bulletin na Oktoban 2026 ya nuna.

 

Binciken ya kuma nuna cewa yawancin manoma na dogaro da kiwo a fili maimakon tsarin kiwon shanu na musamman domin samar da nono.

 

Haka kuma, kashi 97 cikin 100 na gidajen na amfani da hannu wajen tatsar nono, yayin da kashi uku kacal ke amfani da injin tatsar nono, lamarin da masu binciken suka ce na iya ƙara wahalar aiki da haɗarin gurɓacewar nonon.

 

Game da inganta kiwon, binciken ya gano cewa kusan gidaje shida cikin 10 na amfani da hanyoyin gargajiya wajen haɗa shanu domin hayayyafa, abin da ke rage ikon manoma na zaɓen bijimai masu kyau tare da ƙara yiwuwar haɗa shanu masu alaƙar jini.

 

Masu binciken sun ba da shawarar inganta dabarun kiwo, horas da manoma da samar musu da ingantattun shanu domin ƙara yawan nono, kuɗin shiga da kuma wadatar abinci.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *