Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce jam’iyyar ta gudanar da taron tattaunawa da jama’a a yankin Oregun da ke Jihar Legas duk da barazanar kai wa mahalarta hari da kuma tarwatsa taron.
Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan halartar taron ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce ya samu labarin cewa wasu ’yan bangar siyasa sun tattara kansu domin kai wa mutanen da suka isa wurin taron hari.
Ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan siyasa, yana mai cewa tashin hankalin da wasu ’yan siyasa ke ƙarfafawa ba ya amfanar kowa, kuma zai iya shafar al’umma baki ɗaya. Ya jaddada cewa NDC za ta ci gaba da bin doka duk da tsokana da barazanar da take fuskanta.
- Kotu taba INEC sa’o’i 24 ta sanya sunan Adebutu a cikin jaddawalin ‘yan takara
- Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa magoya bayan NDC a Legas
Obi ya ce mahalarta taron sun gabatar da tambayoyi kan farfaɗo da tattalin arziki, rage tsadar rayuwa, yaƙi da cin hanci da rashawa, magance matsalar tsaro da kuma inganta rayuwar talakawa. Ya kuma bayyana manufofinsa na inganta kiwon lafiya da ilimi da kuma rage talauci.
Game da zaɓe mai zuwa, Obi ya jaddada cewa kare sahihancin zaɓe nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, tun daga rumfunan zaɓe zuwa tattara sakamako a matakin gunduma da na ƙarshe.
Ya ce NDC za ta tura ƙwararrun wakilai domin sa ido da tattara bayanan yadda aka gudanar da zaɓe.
Ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar su guji tashin hankali, amma su kasance cikin lumana, masu sanya ido da kuma tsayin daka wajen kare haƙƙinsu na dimokuraɗiyya. Obi ya kuma gode wa waɗanda suka shirya taron, ’yan takarar jam’iyyar a Legas da kuma al’ummar jihar bisa halartar taron.