Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC-PCC) ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da haddasa da ƙarfafa tashe-tashen hankulan siyasa da ake samu a sassan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ADC ta bayyana Allah-wadain da APC-PCC ta yi kan hare-haren da ake kai wa jam’iyyun adawa a matsayin munafunci da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a.

Majalisar ta ce APC da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba za su iya kauce wa alhakin yanayin tashin hankalin siyasa da ke barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar ba.

Ta kuma zargi gwamnonin APC da hana jam’iyyun adawa wuraren taro, rushe ofisoshinsu, kai musu hare-hare da lalata motocin mambobinsu.

ADC ta danganta tarwatsa taron tattaunawar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis a Legas da abin da ta kira dabarun APC na tsoratar da abokan hamayya.

Ta kuma zargi APC da hana jam’iyyun adawa gudanar da kamfen cikin ’yanci ta hanyar takaita liƙa fastoci, sanya allunan tallata ’yan takara da shirya tarukan siyasa, tare da kakaba musu kuɗaɗen da ta ce ba za su iya biya ba.

ADC ta kuma yi zargin cewa ana kai wa mambobinta hare-hare da lalata allunan tallan jam’iyyarsu a wasu jihohi.

Majalisar ta buƙaci Shugaba Tinubu ya tabbatar da gudanar da harkokin siyasa cikin zaman lafiya da haƙuri, tana mai cewa tana tattara bayanan hare-haren da take zargin an kai wa mambobinta domin miƙa su ga hukumomin shari’a da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa.

Ta jaddada cewa ba za ta daina gudanar da kamfen bisa manufofi da batutuwan da suka shafi ƙasa ba duk da zarge-zargen barazana da take yi wa APC.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *