Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanya hannu kan wata doka wadda ke bukatar takaita aikin masu baburan haya da aka fi sani da “Acaba” daga karfe 5:30 na safe zuwa karfe 10:30 na dare a fadin jihar.
Dokar mai taken “Rajistar dole da bin ka’idojin Sufuri a Jihar Oyo” an samar da ita ne domin kara karfafa tsarin tsaron jihar da kuma inganta aiwatar da dokokin zirga-zirga a kan hanyoyin Jihar.
Gwamna Makinde ya ce kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu, musamman sace dalibai da aka yi kwanan nan a Karamar Hukumar Oriire, ya zama wajibi a kara karfafa tsarin tsaron jihar domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- NCDC ta tada hankali kan barazanar Ebola a Najeriya
- Gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da murkushe ‘Yan Ta’adda
- Abuja: ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Banga
Gwamnan ya bayyana bakin cikinsa game da ci gaba da kasancewar wadanda aka sace a hannun masu garkuwa ba’a kai ga kwato su ba.
Makinde ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba dayin duk mai yiwuwa wajen ganin an kubutar da su cikin koshin lafiya.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu taka-tsantsan, hadin kai da jajircewa, yana mai gargadin cewa barin tsoro ya mamaye zukata na iya raunana kwarin gwiwar al’umma wajen fuskantar kalubalen tsaro.
Gwamnatin Jihar dai na cigaba da fuskantar matsin lamba daga iyayen yaran da aka kwashe da kuma al’ummar gari, dake nuna alamun gajiyawa da gwamnatin jihar ke dauka kwanaki sama da 10 da sace yan Makaranta.
