Rahotanni sun nuna hadurran motocin Dangote sun ragu da kashi 56 cikin dari.

Kamfanin simintin Dangote ya fadada amfani da fasahar (AI) domin bibiya da kuma inganta tsaro a harkokin sufurin sa.

Kamfanin ya ce sabbin tsare-tsaren sun hada da horas da direbobi, sa ido kan motocin kamfani da kuma tabbatar da bin ka’idojin hanya.

Shugaban Sashen Sufuri, Murilo Silva, ya ce an samar da sabbin na’urorin bibiya na GPS/Telematics domin lura da tukin direbobi da rage hadurran hanya.

Ya kara da cewa kamfanin ta wayar da kan direbobi kan illar tuki cikin gajiya tare da karfafa hadin gwiwa da hukumomin tsaro da masu motocin daukar kaya.

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta ce hadduran da motocin kamfanin ke yi a baya sun ragu da kashi 56 cikin dari, daga shekarar 2025 zuwa 2026.

A baya bayan nan kamfanin simintin ya koma amfani da motocin dakon kaya dake amfani da Iskar Gas ta (CNG), da motocin daukar kaya na zamani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *