Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin Amurka sun sanar da shi cewa Iran ta harbo jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin kasar kirar Apache wanda ya fadi a gabar tekun Oman.

Cikin wani sako da Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Talata, ya kara da cewa “ya zama wajibi Amurka ta mayar da martani kan wannan harin.”

Ya kara da cewa, “An sanar da ni cewa Iran ta harbo daya daga cikin jiragenmu masu saukar ungulu na Apache masu matukar nagarta yayin da yake sintiri a Tekun Hormuz,” in ji Trump.

A cewar Trump, matuka jirgin su biyu, sun fice daga cikin sa lafiya ba tare da raunata ba, duk da haka, Amurka za ta mayar da martani kan wannan harin.

Rahotanni na nuni da cewa wani jirgin ruwan Amurka marar matuki ne ya ceto matukan, a lamarin da ya sanya Amurka asarar jirgin samfurin Apache na farko tun bayan da fara yaki da Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *