Amurka ta ce dalilan da suka sanya ta hana alkalin wasa ɗan ƙasar Somaliya damar shiga kasar ta na da alaƙa da batutuwa da suka shafi ta’addanci.
Omar Abdulkadir Artan, FIFA ta ɗauke shi domin zama alkalin wasa a gasar cin kofin duniya a Birnin Miami, ya shafe tsawon Awoyi 11 yana fuskantar tambayoyi daga hukumomi, duk da cewa yana da Bizar shiga Amurka.
- Za mu mayar da martani kan Iran – Trump
- Pakistan: Mutane 11 sun rasu a rikicin ‘yansanda da masu zanga-zanga
- Wasanni: Yohanna Zadok ya koma Brighton
A wata hira da ya yi da jaridar The New York Times, Artan ya bayyana matuƙar rashin jin daɗinsa kan wannan mataki.
“Na yi matuƙar baƙin ciki da wannan hukunci. Ina da dukkan takardun da ake buƙata. Ina da ingantacciyar biza,” in ji Artan.
A wani labarin kuma Firaministan lardin British Columbia, David Eby, ya bayyana cewa zasuyi maraba da Omar Artan idan ya samu izinin shiga kasar Kanada domin Alkalancin wani bangare na wasannin cin kofin duniya.
David Eby ya ce zasu baiwa Artan damar yin alƙalanci a wani bangare na wasannin da kasar zata karbi bakunci a Birnin Vancouver, da zai karbi bakuncin gasar Kofin Duniya ta FIFA ta Shekarar 2026.
