Akalla mutane 11 sun mutu yayin da wasu 70 suka yi raunuka bayan barkewar rikici a tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar Pakistan.
‘Yan sanda a yankin sun ce masu zanga-zangar a ƙarkashin ƙungiyar farar hula ta Awami Action Committee, wadda take gwagwarmayar ƙwato wa yankin ‘yanci ta fuskar siyasa da tattalin arziki, sun taru ne a gaban ɗakin ajiye gawa da ke babban asbitin yankin, inda aka ajiye gawar daya daga cikin su wanda jami’an tsaro suka kashe.
- Najeriya, Nijar da Aljeriya sun kaddamar da aikin Bututun Gas
- Trump ya soki ‘Yan Majalisar Wakilan Amurka
- Ambaliya: Ghana na asarar Dala Miliyan 200 duk shekara -GMet
Kwamishinan ‘Yan Sandan yankin, Sardar Waheed Khan, ya ce su ma masu zanga-zangar sun yi ajalin ‘yan sanda huɗu, lamarin da ya ce ya sa jami’an tsaro yin amfani da ƙarfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Babban Sufeton ‘Yan sanda na yankin Liaqat Malik ya ce ƴan sanda 23 na cikin mutane 50 ɗin da suka jikkata a sakamakon arangamar.
