Modi aboki ne na kusa, kuma abin alfaharari inji Tinubu

Shugaba Tunubu ya mika sakon taya ga Firaministan Indiya, Narendra Modi, bisa tarihi na zama Firaministan da ya fi kowa daɗewa a kan mulki ta hanyar zaɓen dimokuraɗiyya a ƙasar Indiya.

Shugaba Tunubu ya bayyana hakane cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar a Abuja

Sanarwar tace wannan nasara tana nuna irin amincewa da ƙwarin gwiwar da al’ummar Indiya suke ci gaba da nuna wa jagorancinsa na wa’adi uku a jere.

Tunubu ya kara da cewa sadaukarwarsa ga hidimar jama’a, jajircewarsa wajen bunƙasa ci gaban ƙasa, da kuma tasirinsa a fagen shugabanci na duniya na ci gaba da zama abin koyi ga miliyoyin mutane a faɗin duniya.

“Baya ga kasancewarsa babban abokin Najeriya, Firaminista Modi aboki ne na ƙashin kai kuma amintaccen abokin hulɗa wanda koyaushe zan iya dogaro da shi. A tsawon shekaru, na ƙara girmama hikimarsa, jarumtarsa da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da ci gaba da wadata ga al’ummarsa.”

Shugaba tunubu yace a madadin Gwamnatin Najeriya da al’ummar Najeriya, yana yi wa Firaminista Modi fatan samun ƙoshin lafiya, ƙarin hikima da nasara yayin da yake ci gaba da jagorantar Indiya zuwa matakai mafi girma na ci gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *