Kasar Iran ta sanar da sake rufe mashigin Hormuz gaba daya.
Iran, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojin hadin gwiwa ta kasar ta fitar ranar Alhamis.
Rundunar ta hadin gwiwa ta ayyana Mashigin Hormuz a rufe ga dukkan jiragen ruwa, ciki har da tankokin mai da jiragen kasuwanci, tana mai cewa duk wani yunkurin wucewa za a kai masa hari.
-
Erdogan ya nuna damuwa da rikicin Gabas ta Tsakiya
-
Zamu sanya kafar wando da kasar Cuba idan ta sayi karin makamai – Hegseth
Sanarwar ta ce rufe mashigin ya zo ne a matsayin martani ga abin da ta kira da “ci gaba da ayyukan farmaki daga Amurka,” ciki har da hare-harenta a wani lardi da ke kudancin Iran.
Sai dai sojojin Amurka sun karyata ikirarin Iran, suna mai cewa “Jiragen kasuwanci na ci gaba da zirga-zirga a ciki da wajen Mashigin Hormuz”.