Da asubahin ranar Litinin, Kasar Ivory Coast ta doke Ecuador da ci 1-0 a gasar cin Kofin Duniya na 2026 da ke gudana a Amurka, Mexico da Canada.

Dan wasan Manchester United Ahmad Diallo, shine ne ya zura kwallo daya tilo a minti na casa’in don samun nasarar Afirka ta farko. Ivory Coast ce ta biyu a Rukunin ‘E’ yayin da Jamus ke matsayi na farko.

Sai dai a wani wasan, Sweden ta murkushe Tunisia da ci 5-1. Tunisia ta zama tawaga ta biyu da ta sha kashi da kwallaye 5 bayan da Jamus ta yiwa Curacao wankin babban bargo da ci 7-1 a daren Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *