Majalisar Wakilai za ta gudanar da zaman gaggawa a yau Litinin domin nazari kan kudirin dokar da ke neman tsawaita wa’adin aiwatar da ɓangaren ayyukan raya ƙasa na kasafin kuɗin shekarar 2025 da ƙarin watanni uku.
A wata sanarwa da Mukaddashin Sakataren Majalisar, Ibrahim Sidi, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa zaman zai gudana ne da misalin ƙarfe 11 na safiar Litinin 15 ga watan Yuni, domin duba kudirin da ke neman sauya wa’adin daga 30 ga Yuni zuwa 30 ga Satumba, 2026.
Kudirin na da nufin bai wa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati ƙarin lokaci don kammala ayyukan raya ƙasa da kuma amfani da kuɗaɗen da aka ware musu a kasafin shekarar 2025.
- Majalisar Wakilai ta amince da kafa ƴan Sandan Jihohi
-
Majalisar Wakilai za ta yanke hukunci kan ‘yan sandan Jihohi
Idan Majalisar Dokoki ta amince da kudirin kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kansa, hakan zai ba da damar ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na ƙasar nan har zuwa ƙarshen watan Satumba.
Masu sa ido kan harkokin gwamnati na ganin cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da cewa an kammala ayyukan ci gaba da aka fara ba tare da an yi watsi da su ba.
