Wata Tawagar Hedikwatar tsaro ta kasa ta isa birnin Katsina domin ta’aziyya ga gwamnatin jihar bisa rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar Mai ritaya.
Shugaban tawagar Manjo Janar IM Abdullahi ya bada tabbacin hedkwatar ta lashi takobin zakulo wadanda ke da alhakin kisan.
- Manyan hafsoshin sojin Najeriya da matsalar tsaro ta rutsa da su
- Hare-haren Boko Haram a yankunan Chibok na neman dawowa
- Ministan Tsaron Najeriya ya ce matsalar tsaro a cikin Al’umma take
Mataimakin gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal, ya ce gwamnatin su zata bayar da dukkanin goyon bayan da Hedikwatar tsaron ke buƙata, domin cimma wannan nasara.
Mal Faruk Lawal ya bayyana cewa gwamnatin Jihar na iyakacin kokarin ta, sai dai ta na buƙatar tallafi daga hukumomin tsaro domin fatattakar bata gari.
A ranar Asabar 13 ga watan Yuni ne Gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar Manjo Rabe a hannun ƴan bindiga, bayan gaza cimma matsayar sako musu ƴan uwa da aka kama a matsayin musaya.
Al’ummar ƙananan hukumomin jihar Katsina sun shafe tsawon lokaci ƙarƙashin matsin ƴan bindiga dake sace su domin karɓar kuɗin fansa.