A ranar Jumma’a, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadi cewa annobar Ebola na yaduwa zuwa sabbin yankuna a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kwango, fiye da yadda aka gano a baya.

Hukumar tace akwai buƙatar ruɓanya ƙoƙarin da ake yi matuƙar ana da burin daƙile ƙwayar cutar daga saurin yaɗuwar ta.

Tun bayan da aka bayyana barkewar cutar a ranar 15 ga Mayu, an samu mutane 676 da aka tabbatar sun kamu da Ebola, ciki har da mutuwar mutane 136, kamar yadda alkaluman WHO na baya-bayan nan suka nuna.

Akwai kuma wasu mutane 119 da ake zargi, yayin da marasa lafiya 32 suka warke.

Babu ingantattun alluran rigakafi ko magungunan da aka amince da su don magance nau’in kwayar cutar Bundibugyo da ke haddasa wannan barkewar cutar, wacce ta fi kamari a lardin Ituri, tare da samun masu dauke da cutar a lardunan Arewaci da Kudancin Kivu.

“Barkewar cutar na ci gaba da fadada ta fuskar yawan masu kamuwa da kuma yadda take yaduwa zuwa wasu wurare,” in ji Olivier le Polain, shugaban bangaren ɗaukin gaggawa na WHO.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *