Babban Hafsan Sojan Najeria Laftanar Janar Waidi Sha’aibu, ya hori Jami’an ɓangaren ƙirƙira na rundunar su ruɓanya ƙoƙarin su.
Babban Hafsan ya yi wannan jan hankalin ne yayin bikin buɗe Makon horo na shekarar 2026, wanda aka fara gudanarwa daga Talata 2 zuwa Alhamis 5 ga Yuni, 2026 a Ibom Hall, Uyo, Jihar Akwa Ibom.
Da yake jawabi a madadin Babban Hafsan, Kwamandan Mulki na rundunar Manjo Janar Adewale Adekeye, ya jinjina wa sashen, kan ci gaban da ake samu wajen kirkire-kirkire, bincike, warware matsaloli a aikace ta hanyar amfani da fasahohi a cikin gida.
Ya nuna cewa irin wannan ƙoƙari na nuna jajircewar Sojan Najeriya wajen ƙarfafa tasirin aiki ta hanyar amfani da dabarun cikin gida, da suka dace da yanayin tsaron ƙasa.
“Taken Makon ya zo dai-dai da burin sauya rundunar Sojan Najeriya zuwa ƙwarewa, shirin ko-ta-kwana, yaƙi da juriya.” Inji Adekeye.
Taken makon na wannan shekarar shine, “Ƙarfafa zukata da Juriya domin tallafawa yaƙi ta hanyoyin kirkire-kirkire a cikin gida, da haɗin gwiwa a aikin Soja.
