Alkalin wasan kwallon kafa dan kasar Somalia, Omar Abdulkadir Artan, wanda aka hana shiga Amurka don yin alkalanci a Kofin Duniya, zai karbi cikakken albashinsa na gasar.

Gwamnatin Trump ta ce Amurka ta hana Artan shiga gasar Kofin Duniya saboda zargin dangantakar sa da kungiyoyin “ta’addanci,” zargin da ya shaida wa Amurka cewa bai san komai game da kungiyar ba.

“Ina da takardun da suka dace da kuma komai. Ina da bizar da ta dace,” in ji Artan-

“Ni alkalin wasa ne kawai da ke kokarin cimma burinsa, babban burin rayuwata, shi ne zuwa Kofin Duniya,” in ji Artan.

Wata majiya da ke da sani kan lamarin ta ce ko da yake Artan ba zai shiga gasar ba, FIFA ta dauki alkawarin biyan albashin sa.

Artan, gwarzon alkalin wasa na Afirka na shekarar 2025, an shirya ya zama dan Somalia na farko da zai yi alkalanci a wannan babban taron kwallon kafa na duniya kafi gamuwa da cikas.

Duk da haka, ya koma gida inda aka tarbe shi kamar gwarzo yayin da hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta bayyana cewa zai yi alkalancin a wasanin UEFA Super Cup tsakanin Paris St Germain da Aston Villa a watan Agusta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *