Akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon hare-haren da Rasha ta kai a Ukraine, yayin da wani hari ya janyo mummunar barna ga babban Cocin Dormition Cathedral mai tarihi da ke Birnin Kyiv

Jami’an agajin gaggawa a Birnin Kyiv sun shafe sa’o’i suna kokarin kashe gobarar da ta tashi a saman rufin cocin da aka gina tun karni na 11 a safiyar Litinin 15 ga watan Yuni.

Cocin na daga cikin muhimman cibiyoyin addinin Kiristanci na Orthodox a Ukraine, wanda wani shahararren masanin gine-gine dan kasar Italiya Aristotle Fioravanti ya tsara a karni na 11.

Babban Daraktan Gidan Tarihi na Kyiv-Pechersk Maksym Ostapenko, ya shaida wa gidan talabijin na gwamnatin cewa wani jirgin yaki mara matuki na Rasha ne ya kai harin kunar bakin wake kan Cocin, lamarin da ya haddasa gobara.

Malaman addini da ma’aikatan ceto sun hada kai wajen kwashe gumaka da kayayyakin tarihi masu matukar daraja daga cocin kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kan wutar.

Ma’aikatar Al’adu ta Ukraine ta ce harin ya kuma yi barna mai yawa a tare da lalata babbar ma’ajiyar kayan sawa ta fina-finai tare da kone tarin kayan tarihi da ba za a iya maye gurbin su ba.

Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko, ya ce kimanin mutane 20 sun jikkata a babban birnin, ciki har da wani yaro da mace mai juna biyu.

Sannan harin ya shafi Sanannen gurinj tarihin nan da ake yiwa lakabi da Kyiv-Pechersk Lavra ko (Monastery of the Caves), sanannen wurin ibada a Gabashin Turai da ke kallon Kogin Dnipro.

Wurin yana dauke da manyan koguna na karkashin kasa masu tsawon fiye da mita 600, kuma ya kasance cibiyar ziyarar masu ibada na tsawon daruruwan shekaru.

Harin na Rasha ya shafi sanannun wurare ne mafi tarihi a kasar, da ake ibadu a cikin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *