Majalisar ECOWAS, za ta fara wani taron mako guda a ranar Litinin 15 ga watan Yuni a Birnin Dakar, domin tattaunawa kan kalubalen amfani da makamashin samar da Lantarki a Yammacin Afirka.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi 14 ga watan Yuni, ta ce taken taron shi ne: “Amfani da Makamashi wajen samar da Wutar Lantarki a Karkara, domin karfafa tattalin arziki a Yankin ECOWAS: Rawar da Majalisar Dokokin ECOWAS za ta taka.”
- Hedikwatar tsaron Najeriya ta lashi takobin zaƙulo waɗanda suka kashe Janar Rabe
- Yadda muke son Rundunar Sojan Najeriya ta koma-Waidi Sha’aibu
- Manyan hafsoshin sojin Najeriya da matsalar tsaro ta rutsa da su
Ana sa ran taron zai samar da sabbin dabaru da tsare-tsare na fadada amfani da sabbin hanyoyin amfani da makamashi domin samar da wutar lantarki cikin hanzari a yankunan karkara.
Taron zai gudana ne da hadin gwiwar kwamitocin akamashi da ma’adinai, noma da muhalli da albarkatun Kasa, da Kwamitin ababen more rayuwa na Majalisar.
Ana sa ran mahalarta taron za su hada da ‘yan majalisar yanki na ECOWAS, wakilan hukumomin ECOWAS, jami’an gwamnati, masu zaman kansu, kungiyoyin fararen hula da kuma kwararrun masana.
ECOWAS ta kuduri aniyar samar da damar samun makamashi mai dorewa kuma mai arha ga kowa nan da shekara ta 2030, kuma ana ganin matakan da majalisar dokoki za ta dauka na da muhimmanci wajen cimma wannan buri.
Daya daga cikin manyan abubuwan da za su gudana a taron shi ne ziyara zuwa wani wuri da ake aikin makamashi a Senegal, inda ‘yan majalisar za su gana kai tsaye da al’ummomin da ke amfana da aikin, ‘yan kasuwar yankin, Mata da Matasa.
Ana sa ran wannan ziyara za ta ba su damar ganewa idanunsu yadda samar da wutar lantarki a karkara ke canza rayuwar al’umma da kuma karfafa harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
A karshen taron na mako guda, ana sa ran mambobin majalisar za su amince da wasu shawarwari da za su taimaka wajen karfafa shirye-shiryen samar da wutar lantarki a karkara, jawo karin zuba jari da kuma inganta sa ido kan aiwatar da manufofi da shirye-shiryen makamashi na ECOWAS.