Mashigar Hurmuz

Ana sa ran buɗe wata tattaunawar kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a ƙasar Switzerland, game da matakin sake rufe mashigar Hormuz da Iran tayi.

A ranar Asabar 20 ga watan Yunin shekarar 2026 ne rundunar sojan Iran ta sanar da sake rufe Mashigar ruwan, biyo bayan wasu jerin hare-hare da Isra’ila ta kai kudancin Lebanon.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya isa ƙasar Switzerland da safiyar Lahadi 21 ga watan Yuni, domin sake buɗe tattaunawar.

Tawagar Iran da ta haɗa da Kakakin Majalisar Dokokin ta Mohammad Bagher Ghalibaf, da Ministan Harkokin Waje, Abbas Araghchi, sun isa ƙasar a daren Asabar.

Ana sa ran Jami’an Amurka dana Iran za su halarci tattaunawar tare da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da Babban Hafsan Sojojin ƙasar, Field Marshal Asim Munir

Pakistan ta taka muhimmiyar rawa a matsayin mai shiga tsakani tun a lokacin yaƙin, wanda har ta karɓi baƙuncin wani zagayen tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a baya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana a cikin wata sanarwa cewar Pakistan za ta ci gaba da tallafa wa tabbatar da fahimtar juna tsakanin ƙasashen Biyu.

JD Vance ya ce yana fatan samun ci gaba kan batun shirin nukiliyar Iran da kuma batun tsagaita wuta a Lebanon.

A farkon wannan makon, shugabannin Amurka da Iran sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta farko da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙin nan take, ciki har da rikicin Lebanon.

Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi alƙawarin ci gaba da tattaunawa domin cimma cikakkiyar yarjejeniya cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Sai dai rikicin da ke ci gaba tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran, wadda ke da sansani a kudancin birnin Beirut na Lebanon, na ƙara dagula lamarin

A ranar Asabar, aƙalla mutane 47 ne suka mutu a Lebanon sakamakon jerin hare-haren sama da Isra’ila ta kai, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *