A ranar Litinin, Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa zai sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar Labour da firaminista, wanda hakan ya kawo ƙarshen watanni na rikicin siyasa tare da buɗe gasar maye gurbinsa.
Sanarwar ta biyo bayan matsin lamba da ke ƙaruwa kan firaministan bayan jam’iyyar Labour ta sha kaye a zaɓukan ƙananan hukumomi a watan Mayu kuma tana fuskantar tawaye mai ƙarfi daga ‘yan majalisar dokokinsa kan shugabancinsa da manufofinsa.
Starmer ya kara da cewa ya yi magana da Sarki Charles da safiyar ranar Litinin, domin sanar da shi matsayar da ya yanke ta yin murabus.
- Hormuz: Iran da Amurka zasu koma teburin sulhu
- Amurka ta kaddamar da sabon jirgin saman da Qatar ta bata kyauta
Kazalika, ya nemi Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar Labour da ya tsara jadawalin lokaci za a buɗe damar gabatar da sunayen sabbin shugabanni a ranar 9 ga Yuli, kuma a kammala kafin dawowa daga hutu.
Wannan na nufin cewa za a samu sabon Firaiminista kafin Majalisa ta dawo daga hutu a watan Satumba.
Starmer, ya ce zai ci gaba da zama a muƙaminsa na firaminista har zuwa lokacin da sabon Firaiministan zai karbi aiki.