Wata mata mai suna Ummulkhairi ta rasa ranta a hannun wasu fusatattun matasa wadanda suka kuma ƙona gawarta a Maraban Jos da ke Jihar Kaduna, bisa zargin cewa mai satar yara ce.
Wani dan jarida da yake bibiyar lamarin ya tabbatar wa Blueprint Radio cewa matar tana kan hanyarta ta zuwa wani taron wa’azi da aka gayyace ta ne, amma saboda ba ta san wurin ba ta tsaya tana tambayar hanya.
“A nan ne wasu suka fara yi mata ihu tare da zargin ta da satar yara, lamarin da ya kai ga taruwar jama’a,” inji shi.
Ba wannan ba ne karo na farko da aka taba kashe mutanen da ba a tabbatar da laifi a kansu ba bisa wasu zarge-zarge.
- Wani harin kwanton bauna ya yi sanadin mutuwar sojoji 7 a Kaduna
- Cunkoso: Hukumar Kiyaye Haddura ta shawarci masu bin hanyar Kaduna
Dan jaridar da muka tattauna da shi ya kara da cewa ko da yake ’yan sanda sun kwato Ummulkhairi sun kai ta ofishinsu, matasan sun bi ta har can, inda suka jefe ta har sai da ta mutu.
Ya kuma ce matasan sun yi wa wani abokin aikinsa da yake daukar waki’ar da waya jina-jina bayan sun yi zargin cewa shi jami’in tsaro ne na farin kaya.
“Da kyar aka samu aka kwato shi a hannunsu, duk fuskarsa ta daddauje,” a cewar dan jaridar.
Mijin Malama Ummulkhairi, Malam Aliyu, ya ce maidakin tasa ta fita daga gida cikin ƙoshin lafiya bayan ta nemi izininsa domin halartar taron wa’azin.
A wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa na zamani, Malam Aliyu ya bayyana yadda aka kira aka sanar da shi game da faruwar wannan lamari.
“Na ga wata bakuwar lamba ta kira ni, sai na ji muryar wani mutum… ya ce an samu masala fa, matarka ta zo da sunan tana neman [wata] makaranta za ta je wa’azi, amma mutane sun kama ta suna zarginta da ta saci yara.
“Sai na ce inna lillahi wa inna illaihi raji’un, sai na ce makarantar Malama Mardiya ke nan.
“Sai ya ce wannan abun fa ba karamar magana ba ce, idan ina da wakili na yi sauri na aiko shi,” inji Malam Aliyu.
Wani malaminta ma ya tabbatar da cewa Ummulkhairi malamar makaranta ce kuma ɗalibarsa, yana mai cewa ya je ofishin ’yan sanda domin ba da shaida a kanta amma hakan bai samu ba.
“Kafin in kammala jawabina, har matasan sun fi karfin hukuma suka kashe ta, har ma suka ƙona mashin ɗin da na hau zuwa wurin,” inji Malam ….
Da muka tutube shi don neman tabbaci game da wannan lamari, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna , ASP Mansir Hassan, ya ce yana wani taro idan ya kammala zai tuntube mu.
Wannan lamari dai yana faruwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya, musamman a Arewa, ciki kuma har da wasu sassan Jihar Kaduna.
Ba kuma shi ne karo na farko na da mutane suka dauki doka a hannu suka hallaka wanda aka zarga ba tare da bincike ba balle tabbatar da sahihancin zargin.