Daga Ibrahima Yakubu
Sau da dama ana tattauna sauyin yanayi ne ta fuskar ƙaruwar zafin duniya da narkewar ƙanƙara, da kuma tsananin sauye-sauyen yanayi. Amma bayan waɗannan bayanai da ƙididdiga, akwai wata illa mai taɓa zuciya: yara da ke tasowa ba tare da iyayensu ba saboda sauyin yanayi ya sa wuraren zamansu suka zama marasa anfani ga rayuwa.
A yankuna da dama da fari, ambaliya da yaɗuwar hamada da lalacewar amfanin gona suka shafa, iyalai suna fuskantar matsalolin da ke tilasta musu yanke shawara masu wahala. Lokacin da ƙasa ta daina ba da amfanin gona ko kuma kifaye suka daina samuwa a ruwa, iyaye kan yi hijira domin neman aiki da hanyar rayuwa. Wasu sukan koma birane, wasu ma su ƙetare iyakoki zuwa wasu ƙasashe. Suna yin ayyuka marasa tabbas kamar aikin gini da aikin gida, ko ƙananan sana’o’in kasuwanci.
Abin da suke bari a baya ba ƙasa da dukiya kaɗai ba ne, har ma da yaransu. Waɗannan yara sukan kasance a hannun kakanni da dangin uwa da uba, ko kuma wani lokaci su riƙa kula da kansu.
Ana ƙara kiran irin waɗannan yara da suna “Marayun Sauyin Yanayi” (Climate Orphans), duk da cewa mafi yawansu iyayensu suna raye. Wannan suna yana bayyana wani yanayi mai raɗaɗi: rabuwar zuciya da iyaye ba don son rai ba, sai dai saboda lalacewar muhalli da rayuwa ta haifar.
A ƙauyuka, wannan matsala tana ƙara yawaita. Idan damina ta gaza zuwa yadda ake bukata, amfanin gona na shekara guda zai iya lalacewa gaba ɗaya. Ambaliya kuma na iya rushe gidaje cikin sa’o’i kaɗan. Lokacin da irin waɗannan abubuwa suke maimaituwa, matsin tattalin arziki yana fara raba iyalai a hankali.
Iyaye kan yi hijira da fatan za su aika kuɗi gida, amma hijira ba koyaushe take kawo nasara ba. Da yawa suna fama da rashin samun tabbataccen aiki a biranen da suka cika da jama’a, kuma kuɗin da suke aikawa gida kan zama kaɗan ko kuma ba sa zuwa akai-akai.
Ga yaran da aka bari a baya, tasirin wannan yanayi yana da yawa. Kakanni ko dangi na iya kula da su, amma galibi ba su da ƙarfin kuɗi ko lafiya da zai maye gurbin kulawar iyaye gaba ɗaya. Karatu kan samu cikas idan ba a iya biyan kuɗin makaranta ba ko kuma idan ana buƙatar yara su taimaka a gona ko wajen neman abin rayuwa a gida.
- Majalisar Dattawa na shirin sake tattauna ƙudirin kafa ’yan sandan Jihohi a zaman gaggawa
- Me ya sa Keir Starmer ya yi murabus daga mukamin Firayim Ministan Birtaniya?
- Rundunar ’Yan sanda ta yi tir da kisan gilla da aka yi wa wata mata bisa zargin satar yaro
- Firaministan Birtaniya Starmer ya yi murabus
Har ila yau, matsalolin tunani da na zuciya suna tasowa. Yara da dama suna jin kamar an yi watsi da su, suna fama da damuwa da rashin tabbas game da makomarsu. Amma galibi ba a ba waɗannan matsaloli kulawar da ta dace.
Wannan al’amari yana sauya yanayin rayuwar al’umma baki ɗaya. Ƙauyuka suna rasa matasa masu ƙarfin aiki, abin da ke barin tsofaffi da yara kawai. Tsarin zamantakewa da ya ta’allaka da kusancin iyali yana fara rauni. A wasu wurare ma, tattalin arzikin yanki yana durƙushewa saboda ƙarancin ma’aikata da raguwar samar da kayayyaki.
Duk da haka, hijirar da sauyin yanayi ke haifarwa ba labarin asara kaɗai ba ne. Haka kuma tana nuna yadda iyalai ke ƙoƙarin jurewa da daidaitawa da matsalolin muhalli da suka fi ƙarfinsu. Amma daidaitawa bai kamata ya zama dalilin da rabuwar iyali za ta zama al’ada ba.
Hanyoyin Magance Matsalar
Magance karuwar “marayun sauyin yanayi” na buƙatar haɗin gwiwa wajen tinkarar musabbabin muhalli da kuma illolin zamantakewar da hijirar sauyin yanayi ke haifarwa.
- Zuba Jari a Noma Mai Jure Sauyin Yanayi
Ya zama dole a tallafa wa manoma da iri masu jure fari da ingantattun hanyoyin ban ruwa, da wuraren adana amfanin gona da ke jure ambaliya, da dabarun noma na zamani masu dacewa da sauyin yanayi. Wannan zai rage asarar amfanin gona kuma ya taimaka wa iyalai su ci gaba da samun abin rayuwa a gida. Idan samun kuɗin shiga a ƙauyuka ya tabbata, buƙatar yin hijira za ta ragu.
- Ƙarfafa Tattalin Arzikin Ƙauyuka
Gwamnatoci da abokan hulɗar ci gaba su samar da hanyoyin samun aikin yi da ba noma kaɗai ba. Kafa masana’antun sarrafa kayan gona, ayyukan makamashi mai sabuntawa, da ƙananan sana’o’i zai rage matsin tattalin arzikin da ke sa iyaye barin yaransu.
- Faɗaɗa Shirye-shiryen Tallafin Jama’a
Shirye-shiryen bayar da tallafin kuɗi, ciyar da yara a makarantu, da kula da walwalar yara za su taimaka wajen tabbatar da cewa yara a yankunan da sauyin yanayi ya shafa suna ci gaba da karatu kuma suna samun kulawar da suke bukata ko da iyalansu suna cikin matsala.
- Tsara Hijira Cikin Tsaro da Tsari
A inda hijira ta zama dole, ya kamata manufofi su taimaka wajen kiyaye haɗin kan iyali. Wannan ya haɗa da samar da gidaje masu araha, damar ilimi ga yaran masu hijira, da hanyoyin da za su ba iyaye damar tafiya tare da yaransu idan zai yiwu. Hanyoyin hijira marasa tsari da haɗari sukan ƙara tsananta rabuwar iyali da rashin tsaro.
- Ƙarfafa Tsarin Kula da Yara a Matakin Al’umma
Ya kamata gwamnatoci da ƙungiyoyin agaji su tallafa wa cibiyoyin kare yara a cikin al’umma domin sa ido kan yara masu rauni, ba su tallafin tunani da na zamantakewa, tare da taimaka wa kakanni da masu kula da yara kada su ɗauki nauyin su kaɗai.
- Sanya Bukatun Yara a Cikin Shirye-shiryen Daidaitawa da Sauyin Yanayi
Dole ne manufofin daidaitawa da sauyin yanayi su ba yara fifiko. Shirye-shiryen sauyin yanayi kada su mai da hankali kan gine-gine da noma kaɗai, su kuma kula da zaman lafiyar al’umma, ci gaban ilimi, da walwalar yara a yankunan da matsalar ta shafa.
Kammalawa
A ƙarshe, rage yawan yaran da ake bari a baya saboda hijirar da sauyin yanayi ke haifarwa na buƙatar kallon sauyin yanayi ba a matsayin matsalar muhalli kawai ba, har ma a matsayin matsalar iyali da zaman lafiyar al’umma.
Kare hanyoyin samun abin rayuwa a yankunan da matsalar ta samo asali, tallafa wa iyalai yayin da suke fuskantar sauye-sauye, da tabbatar da walwalar yara ya zama wajibi. Wannan ne zai ƙayyade ko daidaitawa da sauyin yanayi zai haifar da juriya da ci gaba, ko kuma zai ƙara haddasa tarwatsewar zamantakewa.
Yaran da aka bari a baya ba wai kawai waɗanda hijira ta shafa ba ne; su na tunatarwa cewa sauyin yanayi yana da tasiri mai zurfi ga rayuwar iyali da makomar al’umma baki ɗaya.