Kamfanin Meta ya sanar da cewa shugaban manhajar WhatsApp, Will Cathcart, ya sauka daga mukaminsa bayan shafe shekara bakwai yana jagorantar manhajar.
A cikin wata sanarwa, da shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya ce gudummuwar da Will Cathcart ya bayar na daga cikin abubuwan da suka kai ga bunkasar Manhajar.
Zuckerberg yace yanzu haka WhatsApp na da sama da mutane Biliyan uku dake amfani da Manhajar a duniya, wadda ke ba da fifiko ga kare sirrin masu amfani da ita.
-
Amurka ta kaddamar da sabon jirgin saman da Qatar ta bata kyauta
-
Firaministan Birtaniya Starmer ya yi murabus
Kamfanin ya ce yana matukar godiya ga irin hadin gwiwa da gudunmawar da tsohon shugaban ya bayar, tsawon shekarun da ya yi a kan mukamin.
Sai dai sanarwar ta ce Will Cathcart ba zai bar Meta gaba daya ba, domin zai koma wani sabon matsayi a cikin kamfanin inda zai mayar da hankali wajen kirkiro sabbin abubuwan da zasu amfani al’umma anan gaba.
Hakazalika, kamfanin ya sanar da cewa Kunal Shah zai zama sabon shugaban Manhajar ta WhatsApp.
Meta ta yi karin bayanin cewar, Kunal Shah ne ya kafa fasahar CREED a kasar Indiya, wanda ya zama daya daga cikin manyan kamfanonin fasaha a Indiya da zai goga da saura.
Kunal na da kwarewar kirkire-kirkire da hangen nesa da za ta taimaka masa wajen jagorantar WhatsApp, wadda ita ce mafi girman manhajar aika sakonni a duniya a cewar Meta.
Kamfanin ya bayyana cewa yana sa ran ci gaba da hada kai da Kunal Shah domin tabbatar da cewa WhatsApp ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin muhimman hanyoyin sadarwa ga biliyoyin mutane da kuma miliyoyin kamfanoni a fadin duniya.
