Dakarun Operation Fansar Yamma sun yi nasarar tarwatsa wani sansanin ‘yanta’adda a ƙaramar Hukumar Matazu ta Jihara Katsina tare da hallaka biyu daga cikinsu.

A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar, yace dakarun sun kai wanna samamen ne da sanyin safiyar ranar 22 ga Yuni, 2026 bayan samun wasu bayanan sirri

Yayin samamen dai dakarun sun kashe ‘yan ta’adda biyu, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan bindiga daban-daban

Kazlika dakarun sun kwato Bindiga kirar PKT guda ɗaya da Bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya tare da alburusai da babura guda uku da na’urorin sadarwa da dabbobin da aka sace da kuma sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci

A wani labarin kuma, dakarun sun kashe wasu ’yan ta’adda, sun daƙile wani hari da ake shirin kaiwa, tare da kwato makamai da dabbobin da aka sace ta hanyar jerin hare-haren haɗin gwiwa da suka kai a jihohin Sokoto.

Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da gudanar da hare-hare masu ƙarfi domin rusa duk wata hanyar sadarwar ’yan ta’adda da hana su gudanar da ayyukansu da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a yankin Arewa maso Yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *