Kungiyar Mata ‘Yan Jarida reshen Jihar Kaduna ta raba kunzugun Mata ga dalibai
An sake jaddada bukatar iyaye su rika kula da tsaftar al’adar watan ‘ya’yansu mata a gida akai-akai.
Shugabar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ) reshen Jihar Kaduna, Hajiya Sahura Jibril Maidoki ce ta bayyana hakan yayin wani shirin wayar da kan dalibai tare da rabon kayan tsaftar mata ga daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Asmau Ahmad Makarfi da ke Unguwar Kanawa a Kaduna.
-
Rundunar ’Yan sanda ta yi tir da kisan gilla da aka yi wa wata mata bisa zargin satar yaro
-
Rundunar ’Yan sanda ta yi tir da kisan gilla da aka yi wa wata mata bisa zargin satar yaro
Shirin wayar da kan daliban, wanda ya hada dalibai daga sassa daban-daban na makarantar, ya mayar da hankali ne kan muhimmancin kula da tsaftar al’adar wata da kuma tsaftar jiki ga ‘yan mata masu tasowa.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar kungiyar NAWOJ ta Jihar Kaduna, Hajiya Sahura Jibril Maidoki, ta ce an shirya wannan shiri ne domin tallafa wa ‘ya mace ta hanyar fadakar da ita game da lafiyar al’adar wata tare da samar musu da kayan tsafta domin kara himma a kan karatunsu.
Ita ma da take karawa daliban ilimi, jami’ar kula da lafiya daga Hukumar Kula da lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kaduna, Fatima Sani, ta jaddada bukatar ‘yan mata su kasance masu tsafta a kowane lokaci domin kare lafiyar su.
A nasa jawabin, shugaban makarantar, Malam Tsoho Abdullahi, ya yaba wa kungiyar NAWOJ bisa wannan tallafi, inda ya bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma mai anfani ga daliban makarantar.
Wasu daga cikin daliban da suka amfana da tallafin sun gode wa kungiyar NAWOJ bisa wannan karamci da goyon baya da ta nuna musu. An gudanar da wannan shiri ne a matsayin wani bangare na kudurin kungiyar mata yan Jarida domin tallafawa ‘ya mace, tare da samun gudunmuwa da goyon bayan Maidakin Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Uba Sani.