Hukumar alhazai ta Ƙasa NAHCON ta sanar da kammala jigilar dawo da alhazan Najeriya daga ƙasar Saudiyya bayan gudanar da aikin hajjin shekarar 2026, inda jirgin ƙarshe da ke ɗauke da alhazan Jihar Zamfara ya iso Najeriya, ranar 23 ga Yuni, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa kammala jigilar dawowar alhazai ya kawo ƙarshen dukkan ayyukan Hajjin shekara 2026, wanda ya haɗa da kai da kuma dawo da dubban alhazan Najeriya zuwa daga ƙasa mai tsarki cikin nasara.
Sai dai hukumar ta ce har yanzu akwai alhazai ‘yan Najeriya 12 da ke karɓar magani a asibitoci daban-daban a Saudiyya sakamakon matsalolin lafiya.
NAHCON ta ce tana sa ido sosai kan halin da suke ciki tare da shirya yadda za a dawo da su gida Najeriya da zarar an sallame su daga asibiti.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki kan nasarar aikin Hajjin 2026, tare da yaba wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, bisa goyon bayan da suka bayar.
Ya kuma gode wa hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon Hajji da jami’an lafiya da tsaro da kafafen yaɗa labarai da kuma alhazan Najeriya.
A halin yanzu, hukumar ta sanar da fara shirye-shiryen Hajjin 1448H/2027, inda ta umarci hukumomin alhazai na jihohi da masu gudanar da yawon Hajji masu lasisi da su fara dukkan shirye-shiryen da suka dace bisa ƙa’idojin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta gindaya domin tabbatar da ingantaccen gudanar da Hajjin shekara mai zuwa.