Andy Burnham na ƙara kusantar zama Firayiministan Birtaniya na gaba ba tare da hamayya ba bayan da Minista Darren Jones, wanda ake tunanin zai iya zama abokin hamayyarsa, ya ce ba zai tsaya takara ba.

Burnham, tsohon Minista wanda ya yi aiki tun 2017 a matsayin Magajin garin Greater Manchester, ya lashe zaɓe na musamman a makon da ya gabata don samun kujera a majalisar dokoki da nufin ƙalubalantar Starmer kan shugabancin Jam’iyyar Labour da ƙasar baki ɗaya.

Ya zuwa yanzu, ba ya fuskantar wani mai ƙalubalantarsa.

Jones, wanda ke goyon bayan Starmer, an ƙarfafa shi ya tsaya takara don Burnham ya fuskanci kalubale kan manufofinsa a gaban ‘yan majalisar Labour da mambobi.

A halin yanzu, Keir Starmer, wanda ke son barin abinda za a tuna da shi kafin sauka daga mulki, zai halarci taron amsa tambayoyin Firaiyiminista na mako-mako a Majalisar kafin ya yi tafiya zuwa birnin Berlin don ganawa da ƙawayen su na Turai don tattaunawa kan matsalolin Ukraine da Gabas ta Tsakiya.

Starmer ya bayyana shirinsa na yin murabus ranar Litinin kuma zai bar ofis cikin makonni da zarar jam’iyyar Labour mai mulki ta zaɓi sabon shugaba.

Za a buɗe zaɓen shugabancin Labour ranar 9 ga Yuli kuma a gama bayan mako guda. Idan Burnham ne kawai ɗan takara, zai iya zama firayiminista zuwa 17 ga Yuli.

Idan akwai abokin takara kuma, wanda ya yi nasara zai kama aiki kafin majalisa ta dawo daga hutun bazara ranar 1 ga Satumba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *