kasashen Birtaniya da Najeriya, sun kulla sabuwar yarjejeniya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa kan tallafi da kuma yaƙi da ta’addanci, tsaron yanar gizo, yada labaran ƙarya da sauran ƙalubalen tsaro da ke kunno kai.
An ƙulla yarjejeniyar ne a ranar Talata a ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaron ƙasa Malam Nuhu Ribadu a Abuja.
Taron ya samu halartar Shuwagabannin hukumomin tsaro da na soji ciki har da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, da sauran hafsoshin soji, da kuma jami’an tsaro da na diflomasiyya daga ƙasashen biyu.
-
Hukumar tabbatar da dai-daiton mukamai ta koka da ƙarancin fitowar masu neman aikin soja a Oyo
-
Tinubu ya tura Kudirin ’Yan Sandan Jihohi ga Majalisa
Da yake magana gabanin wata ganawar sirri da jami’an biyu suka yi, Ribadu, ya ce haɗin gwiwar ya shafi yaƙi da ta’addanci, tsaron yanar gizo, zaman lafiyar yankin, tsaron teku, haɗin gwiwar leƙen asiri da sauran matsalolin tsaro.
“Tsarin yakin da matsalar tsaro na zamani ya sha ban-ban da yadda aka saba yi baya, akwai bukatar fasahar samun bayanan sirri,” in ji shi.
A nasa jawaban, mai ba da shawara kan harkokin tsaron ƙasa na Ƙasar Birtaniya, Jonathan Powell, ya bayyana Najeriya a matsayin babbar abokiyar kawancen Birtaniya a Afirka, wadda ta kasance babbar ginshiƙin zaman lafiyar yankin.
“Waɗannan ƙalubalen suna buƙatar mu sauya dabarunmu kuma mu yi aiki tare sosai fiye da kowane lokaci,” in ji Powell.
