Shugaban ya bukaci majalisar ta sahale kudirin ya samu zarcewa ba tare da jinkiri ba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa kudirin sauya kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan jihohi zuwa Majalisar Dattawa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Talata, inda ya ce za a fara duba kudirin a ranar Laraba.

Akpabio ya kuma bayyana cewa jihohi sun yi alkawarin aiwatar da nasu bangaren a ranar da za su karɓi kudirin, domin ba da damar ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin da zai samar da tsarin ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

Kudirin na neman sauya wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 domin samar da tsarin da zai kai ga kafa  ‘yan sandan na jihohi.

Matakin ya biyo bayan kiraye-kirayen Shugaba Tinubu na yin gyare-gyare domin bai wa jihohi damar taka rawa sosai wajen kare yankunansu.

Idan za a tuna, a baya, Tinubu ya buƙaci Majalisar Tarayya ta yi gyaran kundin tsarin mulki domin shigar da batun ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin ta’addanci, ‘yan fashi da sauran barazanar tsaro.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta ɗauki tsauraran matakai kan masu aikata manyan laifuka da masu tallafa musu.

Masu sharhi na ganin kafa ‘yan sandan jihohi na daga cikin manyan sauye-sauyen inganta tsaro da ake shirin aiwatarwa a Najeriya, yayin da Majalisar Tarayya ke ci gaba da duba hanyoyin raba ikon kula da tsaro tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *