Babbar Kotun Jihar Ondo da ke zama a Akure ta yanke ma wasu maza uku, Uche Onu, Ekene Okorie, da Celestine Eze, hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin fashi da makami.

Ana zargin sun aikata laifinne a kamfanin Gasland Nigeria Limited, dake Akure, ranar 25 ga watan Afrilun 2024, da misalin ƙarfe 3:00 na dare, inda suka sace tukunyar gas da wata mota.

An bayyana cewa sun yi galaba a kan mai gadin da ke bakin aiki, inda suka dake shi da wani ƙarfe a kai.

Sai dai kuma mutum ukun da ake tuhumar sun musanta cewa suna da hannu a fashi da makamin.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a William Olamide, ya tabbatar da cewa shaidun da aka gabatar gaban kotu sun tabbatar da faruwar fashi da makami, kana kuma ƴan fashin suna ɗauke da makamai yayin gudanar da fashin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *