Dakarun Rundunar Operation HADIN KAI (OPHK), sun ceto mutane sama da 47, galibin su mata da yara, waɗanda ’yan ta’addan ISWAP suka riƙe a matsayin fursunoni a Kangarwa, Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno, a ranar 20 ga Yuni, 2026

A wata sanarwa da kakakin rundunar Kyaftin Mohammed Goni yace an samu nasarar wannan aikin ceton ne sakamakon ci gaba da matsin lamba da kuma hare-haren da dakarun OPHK ke kai wa maɓoyar ’yan ta’addar ISWAP a yankin Tafkin Chadi

Yace hare-haren ƙasa da na sama da rundunar ke kai wa ba tare da sassautawa ba sun tilasta wa ’yan ta’addan barin sansanoninsu cikin ruɗani da firgici, wanda ya ba wa waɗanda aka tsare damar tserewa daga hannun ‘yanbindigan

A halin yanzu, mutanen da aka ceto suna karɓar kulawar likitoci a wani wuri mai tsaro

Kyaftin Goni yace wannan nasarar ta sake nuna jajircewar dakarun Operation HADIN KAI ba kawai wajen raunana ƙarfin ’yan ta’adda ba, har ma wajen ceto fararen hula marasa laifi da aka tsare ba tare da son ransu ba.

Hedikwatar rundunar ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da kai hare-hare kan ragowar cibiyoyin ISWAP, rusa hanyoyin sadarwarsu da kuma dawo da zaman lafiya da walwala a duk yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *