Tsofaffin manyan hafsoshin soja da ‘yan sanda sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan irin ikon da ya kamata gwamnoni su samu a karkashin sabon tsarin.
Wasu na ganin cewa gwamnoni su samu tasiri mai karfi saboda su ne za su samar da kudaden gudanarwa da kayan aiki, yayin da wasu ke gargadin cewa dole ne a samar da matakan kariya domin hana amfani da rundunar wajen murkushe masu adawa da gwamnati ko tauye hakkin jama’a.
Tsohon Birgediya Janar Peter Aro ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tattara bayanan sirri, saurin mayar da martani ga matsalolin tsaro da kuma bai wa jihohi damar amfani da fasahohin zamani wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
- Tinubu ya tura Kudirin ’Yan Sandan Jihohi ga Majalisa
-
Majalisar Dattawa na shirin sake tattauna ƙudirin kafa ’yan sandan Jihohi a zaman gaggawa
Haka kuma tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Ali Amodu, ya ce tsarin zai taimaka wajen magance kalubalen tsaro cikin gaggawa saboda kusancin rundunar da al’ummomin da take aiki a cikinsu.
Sai dai tsohon DIG Wilson Inalegwu ya nuna damuwa kan yiwuwar cin zarafin iko idan ba a samar da hukumomin sa ido masu zaman kansu ba.
Ya ce ya zama wajibi a tabbatar da cewa rundunar tana aiki ne bisa tanadin doka tare da kare hakkin jama’a ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya aike wa Majalisar Dokoki da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin da zai bai wa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, tare da ci gaba da kasancewar rundunar ‘yan sandan tarayya.
Masu goyon bayan kudirin na ganin zai taimaka wajen yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuka ta hanyar kusantar da harkokin tsaro zuwa matakin al’umma.
Idan kudirin ya samu amincewar Majalisar Tarayya da kuma goyon bayan akalla majalisun dokoki na jihohi 24, zai zama daya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka taba yi a tsarin aikin ‘yan sanda tun bayan samun ‘yancin kai a Najeriya.