Najeriya da Birtaniya sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannin tsaro domin tunkarar sabbin barazanar da ke tasowa a duniya, ciki har da ta’addanci, hare-haren intanet, yaɗa labaran ƙarya da kuma aikata manyan laifukan da suka shafi ƙungiyoyin masu laifi.
Hakan na zuwa ne yayin taron tattaunawar tsaro da tsare-tsare karo na huɗu tsakanin ƙasashen biyu (SDP4) da aka gudanar a Abuja.
Taron ya haɗa manyan jami’an tsaro daga ɓangarorin biyu, ciki har da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da takwaransa na Birtaniya, Jonathan Powell.
Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin haɗin kai da musayar bayanan sirri wajen magance barazanar tsaro da ke ƙara rikicewa.
- Mun rabawa dubban Almajirai Naman Sallah a bana -Hukumar kula da Almajirai
- Najeriya ta fi kowace kasa yawan tamowa a 2025 —MSF
- Sokoto a ƙarfafa yaƙi da mace-macen mata da yara hanyar wayar da kan al’umma
Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro kan Sadarwa da Hulɗa da Ƙungiyoyin Jama’a, Chido Onumah, ya bayyana cewa haɗin gwiwar ya wuce matakin tattaunawa kawai, inda ya koma wani tsari na samar da sakamako a aikace da kuma ƙarfafa cibiyoyin tsaro a ƙasashen biyu.
A cewarsa, haɗin gwiwar ya mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tsaron teku, tsaron intanet, haɗin kan hukumomin tsaro da kuma dakile hanyoyin samun kuɗaɗen haramtattun ayyuka.
Haka kuma, an tattauna yadda za a inganta dabarun sadarwa da kare al’umma daga yaɗa bayanan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya.
Taron ya nuna cewa matsalolin tsaro na zamani na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, hukumomin tsaro, cibiyoyin fasaha da kuma al’umma baki ɗaya.
Najeriya da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da bunƙasa wannan haɗin gwiwa domin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a ƙasashensu da kuma yankin Yammacin Afirka gaba ɗaya.