Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a Kananan Hukumomi 10 na Jihar.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba 24 ga Yunin 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa dokar hana fitar za ta kasance daga karfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe, kuma za ta fara aiki na tsawon sa’o’i 48 a matakin farko.

Ta kara da cewa dokar ta shafi kananan hukumomin da ke makwabtaka da gurin shakatawa na tsohowar Oyo (Oyo National Park).

“Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a ƙananan hukumomi 10 na jihar,” in ji sanarwar.

Farfesa Babatunde ya ce dokar, wadda za ta fara daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe, za ta yi aiki na tsawon sa’o’i 48 da farko, kuma ta shafi yankunan da ke kusa da tsohon gurin shaka tawa na Oyo

Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da Oriire (Ikoyi-Ile) da Orelope (Igboho) da Irepo (Kisi) da Saki ta Arewa (Saki) da Saki ta yamma (Ago-Amodu) da Atisbo (Tede/Ago-Are) da Itesiwaju (Otu- Iseyin (Iseyin) da Olorunsogo (Igbeti).

Hukumar jihar ba ta bayyana cikakken dalilin sanya dokar hana fitar ba a cikin sanarwar da ta fitar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *