An rantsar da sabbin Sanatoci huɗu da aka zaɓa yayin zaɓen cike gurbi na ranar Asabar da ta gabata a zauren majalisar Dattawa.
An zaɓi ‘yan majalisun ne domin wakiltar mazaɓu a jihohin Ondo, Nasarawa, Enugu, da Rivers.
Sabbin ‘yan Majalisun sun haɗa da Farfesa Francis Faduyile (APC, Ondo ta Kudu) wanda ya maye gurbin Jimoh Ibrahim, wanda yanzu shi ne wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, da kuma Barrister Danladi Halilu Envulu-Anza (APC, Nasarawa ta Arewa), wanda ya maye gurbin Sanata Godiya Akwashiki, wanda ya rasu a Disambar 2025.
-
Tsofaffin manyan hafsoshin soja da ‘yan sanda sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan‘yan sandan jihohi
-
An yanke wa ƴan fashi da makami uku hukuncin kisa
Sauran su ne Asogwa Ikeje Israel (APC, Enugu ta Arewa), wanda ya maye gurbin Sanata Okey Ezea, wanda ya rasu a Nuwambar 2025 da Olaka Nwogu (PDP, Rivers ta Kudu maso Gabas), wanda ya maye gurbin Sanata Barry Mpigi, wanda ya rasu a Fabrairun, 2026.
Yayin da yake addu’ar neman Allah ya jikan rayukan ‘yan majalisar da suka rasu, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, wanda ya jagoranci zaman, ya taya sabbin Sanatocin da aka rantsar murna.
